Resumen del episodio
Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan makon zai kai ku kai tsaye zuwa cikin azuzuwan karatu na yankin Afirka ta Kudu da Sahara, yayin da rahoton baya-bayan nan na hukumar UNESCO ya girgiza duniya, inda ya bayyana cewa ana buƙatar ƙarin malamai miliyan Hamsin nan da shekara ta 2030 domin ceto ilimin duniya. Amma abin mamaki da kuma ban tsoro shi ne; kusan miliyan 15 na waɗannan malamai, a nan yankinmu na Afirka ake buƙatarsu. Ku latsa alamar sauti don sauraron shirin tare da Shamsiyya Haruna............
Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan makon zai kai ku kai tsaye zuwa cikin azuzuwan karatu na yankin Afirka ta Kudu da Sahara, yayin da rahoton baya-bayan nan na hukumar UNESCO ya girgiza duniya, inda ya bayyana cewa ana buƙatar ƙarin malamai miliyan Hamsin nan da shekara ta 2030 domin ceto ilimin duniya. Amma abin mamaki da kuma ban tsoro shi ne; kusan miliyan 15 na waɗannan malamai, a nan yankinmu na Afirka ake buƙatarsu. Ku latsa alamar sauti don sauraron shirin tare da Shamsiyya Haruna............
Episodios
Yadda ƙarancin malamai ke barazana ga harkar ilimi a yankin Afrika
EscuchadoShirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan makon zai kai ku kai tsaye zuwa cikin azuzuwan karatu na yankin Afirka ta Kudu da Sahara, yayin da rahoton baya-bayan nan na hukumar UNESCO ya girgiza duniya, inda ya bayyana cewa ana buƙatar ƙarin malamai miliyan Hamsin nan da shekara ta 2030 domin ceto ilimin duniya. Amma abin mamaki da kuma ban tsoro shi ne; kusan miliyan 15 na waɗannan malamai, a nan yankinmu na Afirka ake buƙatarsu. Ku latsa alamar sauti don sauraron shirin tare da Shamsiyya Haruna............
Yadda ambaliyar ta kassara makarantu da dama a arewacin Najeriya
EscuchadoShirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan makon ya duba halin da makarantu ke ciki ne a Tarayyar Najeriya sakamakon fuskantar matsalar ambaliyar ruwa a sassa daban daban na ƙasar.
Najeriya: saɓanin alƙaluma kan jihar da ɗalibanta ke kan gaba a cin jarabawar NECO
EscuchadoA yau shirin zai leƙa Najeriya, inda aka samu saɓani ta fuskar alƙaluma a fannin ilimi, bayan fitar da sakamakon jarabawar ƙasa ta NECO na shekarar 2026, gwamnatin jihar Kano ta sanar da cewa jihar ce ta zo ta ɗaya a fadin ƙasar. Sai dai, wani bincike mai zurfi da jaridar Premium Times ta yi, ya musanta wannan iƙirari, inda ta ajiye jihar a matsayi na 31. Latsa alamar sauti don sauraren shirin...
Jigawa ta gabatar da tsarin rage barace-baracen Almajirai a jihar
EscuchadoShirin Ilimi Hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako ya mayar da hankali kan daɗaɗɗen batun nan na yaran da basa zuwa makaranta a Najeriya matsalar da har kawo yanzu ta ƙi ci taki cinyewa. Wani Rahoton UNICEF ya bayyana jihohin Kano da Jigawa da kuma Katsina a matsayin jihohin da ke da rinjayen yaren da basa zuwa Makaranta, inda a jumlace ƙasar ta yammacin Afrika ke da yara fiye da miliyan 18 da basa zuwa Makaranta, galibinsu a arewacin ƙasar. Tuni Jihar Jigawa ta ɗaura ɗamarar yaƙi da wannan matsala, inda ta gabatar da wani sabon tsarin mayar da ɗimbin yara makarantu. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Gwamnatin Kano na shirin tilasta koyar da ilimin Kwamfuta a makarantun Firamare da Sakandare
EscuchadoShirin Ilimi Hasken rayuwa na wannan mako ya mayar da hankali ne kan yadda majalisar dokoki jihar Kano ta bukaci a mayar da ilimin Kyamfuta dole a matakin makarantun Firamare da Sakandare. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna.